Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da wasu ƴan takarar kujerar kakakin majalisa ta 10.
Shugaban ƙasa Tinubu ya sanya labule da wasu daga cikin ƴan takarar da ke neman ɗarewa kan kujerar da Femi Gbajabiamila zai bari.
Shugaban ƙasar ya sanya labule da biyar daga cikin ƴan takarar guda shida waɗanda suka yi bore kan hukuncin APC da Tinubu na marawa Abbas,/Kalu baya a shugabancin majalisar.
Wannan matsayar dai ta jam'iyyar APC da Tinubu ta kawo rarrabuwar kai a cikin jam'iyyar.
No comments:
Post a Comment